Gwamnatin tarayyar Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce Najeriya ta amince ta shiga sabuwar kungiyar kawancen kasashen duniya saboda cimma burinta na kawar da yunwa da talauci.
Ministan tsaron Najeriya ya ce dakarun sojojin Najeriya sun fara fatattakar ƴan ta'addan Lakurawa, waɗanda suka fara kai hare-hare a jihohin Kebbi da Sokoto.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a samu karin kaso 60 na kudaden albashin ma'aikatan tarayya a shekarar 2025 wand ake nufin cewa ma'aikatan za su kashe N6.5trn.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya domin zuwa kasar Brazil a daren ranar Lahadi. Shugaba Tinubu zai halarci taron kasashen G20 a Brazil.
Olusegun Obasanjo ya caccaki tsarin mulkin Bola Tinubu ya raɗa masa suna Baba go slow. Obasanjo ya ce yana shaida yadda kasa ta rikice a mulkin Bola Tinubu.
Bayan shafe kwanaki biyu ana bukukuwan jana'iza, an birne gawar marigayi hafsan sojojin ƙasa ta Najeriya, Taoreed Lagbaja a gaban manyan ƙasa a Abuja.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa miliyoyin 'yan Najeriya ne za su amfana da shirye shiryen Shugaba Bola Tinubu na dogon lokaci. Minista Mogammed Idris ya fadi haka.
Kotun kolin Najeriya ta raba gardama, ta yi fatali da karar da wasu jihohi a suka kalubalanci halascin kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC.
Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shirin karbo rancen $2.2 biliyan domin habaka tattalin arziki, tare da shirin tallafin gidaje mai rahusa ga ‘yan kasa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari