Gwamnatin Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da rashin wutar lantarki musamman a Arewacin Najeriya inda ya ba da shawarwari.
Matan da za su zama ministoci a gwamnatin Bola Tinubu sun hada da Dr. Suwaiba Said Ahmad. Su ne sababbin matan da suka shiga gwamnatin APC mai mulki.
An kafa kwamiti da zai yi aiki a Majalisa ya yi bincike kan yadda aka dauki ayyuka a wasu hukumomi. Za a gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin makonni hudu.
Akwai wasu lokutan da Sanatan Boro ta Kudu, Ali Muhammadu Ndume ya cire kara, ya soki Bola Tinubu duk da Sanata Ali Ndume ya na cikin jagorori a jam’iyyar APC.
Tsohuwar Ministar mata a gwamnatin Bola Tinubu, Uju Kennedy-Ohanenye ta nuna goyon bayanta wurin taya shugaban inganta Najeriya inda ta ce tana tare da shi.
IMF ya ce babu ruwansa a cire tallafin fetur a Najeriya. Daraktan Afrika na asusun, Abebe Selassie ne ya fadi haka, ya ce amma mataki ne mai kyawun gaske.
Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta dura kan Bola Tinubu kan umarnin ministoci su rage motoci zuwa uku. Kungiyar ta ce Bola Tinubu ne zai fara rage kashe kudi.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ƙaryata rade-radin da ake cewa ya nemi wa'adi na uku a karshen mulkinsa inda ya ce da yana so da ya yi.
Gwamnatin Katsina ta bayyana jin dadin yadda jama'a su ka fara daukar shawarwarinta kare kai daga hare haren yan bindiga da su ka addabi kauyuka da dama.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari