
Gwamnatin Najeriya







Tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh AbdulAziz Dutsen Tanshi.

Shugaban kasar Amurka, Donlad Trump ya bayyana sanya sababbin harajin kaya a kan wasu ƙasashen duniya, a kokarinsa ya tattaro wa kasar karin kudin shiga.

Yayin da Nijar ke ci gaba da fuskantar matsaloli na wahalar mai, Najeriya na kokarin rage wahalhalun tattalin arziki inda take samar da man fetur zuwa kasar.

Gwamnatin jihar Kogi ta musa zargin cewa ta kitsa yadda za ta kashe Sanata Natasha Akpoti. Haka zalika shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio ya musa zargin.

Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kakaba harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga mambobin kasashen ECOWAS ciki har da Najeriya.

Bankin duniya ya amince da ba gwamnatin Najeriya bashin kudi har dala miliyan 500 domin habaka tattali. Za a raba kudin ne wa 'yan kasuwa da gidajen jama'a.

Kungiyar 'yan kasuwar man fetur sun kara kudin litar man fetur a Najeriya. za a dawo sayar da litar mai a N900 a kan N890 da aka saba a makon da ya wuce.

Gwamnatin tarayya ta ƙaryata cewa ana cin zarafin kiristoci a kasar, kamar yadda majalisar Amurka ta bayyana, har ta ke neman a hukunta kasar da takunkumi.

Kasuwar matatar Dangote ta bude a Turai bayan Najeriya ta ki amincewa da cigaban yarjejeniyar sayar mata da danyen mai a farashin Naira kamar yadda aka cimma a baya.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari