Nade-naden gwamnati
Wasu rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi garambawul a mukaman Ministocinsa saboda yadda wasu daga cikinsu ba su tabuka komai ba.
An kawo ma’aikatun Najeriya da aka shafe watanni babu Ministoci a mulkin APC. A yanzu jihar Filato ba ta da ko Minista guda a majalisar zartarwa.
A cikin shekaru kusan 40, mutane da-dama sun jagoranci NIA wajen aikin leken asiri. A rahoton nan, an kawo jerin sunayen daukacin shugabannin hukumar NIA a tarihi.
Mun kawo sunayen shugabannin da hukumar tayi a tarihi daga 1986 zuwa 2024. Shugaban farko da aka yi shi ne Ismail Gwarzo da Ibrahim Babangida ya nada.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi nade nade a gwamnatinsa. Gwamnan na jam'iyyar APC ya nada sababbin manyan sakatarori guda 12 a jihar.
A yayin da hukumar NIMET ta fitar da rahoto kan barnar da ambaliyar ruwa ta yiwa manoma, ministan noma, Abubakar Kyari ya yi magana kan matakin da aka dauka.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Adeola Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) bayan murabus din Yusuf Bichi.
Wasu ‘yan ta'adda da ba a san ko su wanene ba ne sun kai wa kwamishinan muhalli na jihar Oyo, Honarabul Mogbanjubola Olawale Jagaban hari a ranar Litinin.
Kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed ya kwanta dama. An ce ya rasu ne a safiyar yau Litinin, 26 ga Agustan 2024 a cikin gidansa da ke Maiduguri.
Nade-naden gwamnati
Samu kari