Nade-naden gwamnati
Mutanen yankin ƙaramar hukumar Ringim a jihar Jigawa sun yi zanga-zanga a kofar shiga gidan gwamnatin jihar jiya Alhami, sun nemi a tsige kwamishina.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Justice Kudirat Kekere-Ekun matsayin sabuwar shugabar alkalan Najeriya a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.
An ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai Faransa. A zaman majalisar zartarwa ne na yau ake sa ran zai rantsar da Kekere-Ekun.
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce yana da yaƙinin babu mai zarginsa da cin hanci da rashawa ko ya sauka daga mulki, ya nuna yana da rikon amana.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kafa kwamitin mutum 11 karkashin Farfesa Usman Muhammad omin binciken dalilin samun sabani tsakanin Yarbawa da ke zaune a Kano.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya dakatar da manyan jami'an gwamnatinsa mutum hudu. Gwamnan ya dakatar da kwamishinoni biyu da wasu jami'ai.
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya amince da naɗin mutane 1,192 a matsayin masu taimaka masa na musamman, matakin zai fara aiki a watan Satumba.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugaban hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON kan badakalar aikin hajjin bana, ya naɗa Sheikh Farfesa Abdullahi Pakistan.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari gidan wani hadimin gwamnan Katsina inda suka kashe shi da uwar gidansa tare da kuma sace amaryarsa.
Nade-naden gwamnati
Samu kari