Nade-naden gwamnati
Kungiyar matasan yankin da ake hakar mai a Ondo ta bukaci Shugaba Tinubu ya cire Otito Ehinmore daga hukumar NDDC bisa zargin cin hanci da rashin wakilci nagari.
Fayose ya ce Obi ne kadai mai tasiri a ƴan adawa, kuma ADC ba za ta kai labari a 2027 ba, yayin da ya fadi dalilin ƙin karbar tayin mukami da Tinubu ya yi masa.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kori Samson Osagie daga matsayin kwamishinan shari’a, ya kuma ƙara ma’aikatu zuwa 28 don daidaita tsarin gwamnati.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Ministan Kudi Wale Edun ba ya cikin hadari, bayan rahoton rashin lafiyarsa da jita-jitar cewa za a maye gurbinsa.
Minista Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ce auren wuri yana hana ci gaban Najeriya, inda 44% na ‘yan mata ke yin aure kafin shekara 18, bisa bayanan hukumar UNICEF.
Bayan murabus din ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, an samu kofar nadin sabon minista daga Jihar Enugu, inda ake ganin tsofaffin gwamnoni biyu za su nema.
Ministan ma'adanai, Dele Alake ya nunka tsaronsa bayan samun barazanar kisa daga wadanda aka soke wa lasisin hakar ma’adinai, duk da umarnin Shugaba Tinubu.
Kwamitin rikon kwarya da APC ta kafa a jihar Enugu ya tabbatar da cewa Gwamna Peter Mbah da mukarrabansa za su dawo jam'iyya mai mulkin Najeriya a makon gobe.
Sanata Ali Ndume ya ce tantance ministoci ba aikin majalisar dattawa ba ne, bayan rikicin takardun bogi na tsohon minista Uche Nnaji ya jawo cece-kuce.
Nade-naden gwamnati
Samu kari