Labaran Kwallo
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan mutuwar tsohon shugaban CAF Issa Hayatou. Marigayi Issa Hayatou ya rike mukaddashin shugaban FIFA.
Allah ya yi wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka (CAF) Issa Hayatou rasuwa. An ce ya rasu bayan fama da rashin lafiya yayin da zai cika shekara 78.
Rigima ta barke tsakanin Espanyol da tsohon dan wasan kwallon kafa ta Barcelona, Martin Braithwaite inda ya taya tsohuwar kungiyarsa domin siyanta.
An saka 'yar wasan Super Falcons, Asisat Oshoala, da tsohuwar ‘yar wasan Najeriya, Perpetual Nkwocha, cikin jerin ‘yan wasa 25 da suka fi fice a Afirka.
Allah ya yi wa mahaifiyar mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil, Pele, Celeste Arantes rasuwa tana da shekara 101. Ta rasu a ranar Juma'a a Brazil.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanar da mutuwar tsohon dan wasanta, Kevin Campbell bayan fama da jinya yayin da Everton ta tura sakon jaje kan rashin.
Hukumar NFF ta yanke shawarar daukar wani mai hoarar da 'yan wasa daga Turai domin jan ragamar tawagar Super Eagles, sakamakon gazawar Finidi George.
Real Madrid ta kasar Spain za ta kece da Borussia Dortmund ta kasar Jamus a wasan karshe na ɓa neman cin gasar kofin zakarun Turai (UCL) 2024 a Wembley.
Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al Nassr ta sha kashi a hannun Al Hilal a bugun fanariti a wasan karshe na gasar cin kofin sarki a ranar Juma'a.
Labaran Kwallo
Samu kari