Labaran Kwallo
Najeriya da Morocco za su kece raini a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Nahiyar Afrika (AFCON), 2025. Legit za ta kawo rahoton wasan kai tsaye.
Dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen ya bayyana cewa tawagar Super Eagles ba ta jin dar-dar kan karawa da takwararta ta Morocco a gasar AFCON 2025.
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta karfafa gwiwar tawagar 'yan wasan Super Eagles kan wasan da su yi da Morocco.
Jose Mourinho ya yi hasashen cewa Morocco za ta doke Najeriya a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON 2025, inda ya ce Atlas Lions ce ƙungiya mafi tsari a Afirka.
Gasar AFCON 2025 na ci gaba da gudana a kasar Morocco. Akwai wasu zaratan sababbin matasan 'yan wasa da suka dauki hankula. Akor Adams na Najeriya na cikinsu.
Walid Regragui ya bayyana fargabarsa kan Osimhen da Lookman, yayin da yake murnar rashin Ndidi a wasan Najeriya da Morocco na Semi-final a daren yau Laraba.
Morocco za ta rasa Azzedine Ounahi babban dan wasan tsakiyarta, yayin da Najeriya za ta rasa Wilfred Ndidi a wasan semi-final na AFCON ranar 14 ga Janairu, 2026.
Odion Ighalo ya gargaɗi Najeriya ta ƙara kaimi don doke Morocco a wasan semi-final na AFCON ranar Laraba (Jan 14, 2026) a birnin Rabat don kai wa wasan ƙarshe.
CAF ta naɗa Daniel Laryea ɗan Ghana a matsayin alƙalin wasan Najeriya da Morocco na ranar 14 ga Janairu, 2026); an tsaurara matakan VAR don tabbatar da adalci.
Labaran Kwallo
Samu kari