Aikin noma
Kungiyar Manoma a Najeriya (AFAN ) ta bayyana cewa wadanda su ka ci bashin kudaden lamuni na CBN yawanci ba manoma ba ne shi yasa samo kudaden zai yi wahala.
Yayin da barayi su ka yi yawa yanzu wurin satar amfanin gona, wasu manoma sun bayyana yadda su ke biyan kudi tare da kwana a gonaki don gudun satar kayan gona.
Wasu mutane sun kai farmaki rumbun abinci na gwamnati da ke jihar Bayelsa tare da dibar kaya masu tarin yawa, wani abincin ya rube a ajiye tun shekarar 2022.
Wasu magidanta na satar kayyayakin gonar mutane don kai wa iyalansu a jihar Taraba, wasu manoman sun ce ganin halin da ake ciki ba su kai su kara ba ga hukumomi
Za a ga tsadar abinci, buhun shikafa zai kuma tsada a kasuwa. ‘Yan kasuwan da ke Arewa a karkashin NACCIMA sun fara ankarar da al’umma kan halin da ake ciki
Gwamnatin Kano ta bankado wata badakalar makudan kudade a hukumar Samar da Kayan Noma, KASCO a jihar kan karkatar da Naira biliya 4 da aka ware don harkar noma.
Najeriya na kara fadawa matsala yayin da ake samun karuwar samun wasu abubuwan da ke tashi. Yanzu haka an ce wata kwayar cuta ta bullo a kasar tana kama kubewa.
JIhohi biyar ne hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana cewa sun fi kowace jiha a Najeriya sayen kayayyakin abinci da tsada. Cikin jihon akwai jihar Kwara.
Tsadar tumatir ta sanya matan babban birnin tarayya Abuja komawa amfani da karas da wasu nau'o'in kayan lambu wajen yin miya saɓanin tumatir da aka saba amfani.
Aikin noma
Samu kari