Malaman darika
Kotun jihar Kano ta sassautawa Sheikh Ibrahim Abdullahi Isa Makwarari sharudan beli bayan shafe mako biyu ba tare da cika sharudan da aka kafa masa ba.
Sheikh Khalifa Usman Kusfa (Rigi-rigi) ya rasu a Kaduna; za a yi jana'izarsa a Zaria a yau 2 ga Fabrairu, 2026. Duniya ta yi rashin babban malami mai son Annabi.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Kusfa Zariya ya rasu bayan fama da doguwar jinya a Kaduna. Malamin ya shahara da wa'azi a kafafen sadarwa.
Gwamnan jihar Bauchi ya amince da tsarin sanya limamai da fastoci samun alawsu duk wata. Gwamnati za ta rika biyansu ba tare da nuna bambanci ba.
Kotu ta tura malamin Musulunci, shugaban tsagin Darikar Qadiriyya, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari gidan gyaran hali kar karkatar da fili bayan gaza cika sharudan beli.
An gurfanar da malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a kotun Kano kan zargin karkatar da filayen gwamnati da na al'umma. Ana zargin shi da laifuffuka.
Mabiya Tijjaniyya miliyan 3 sun hallara a Katsina domin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass; Gwamna Radda da Sarki Sanusi sun yi kira ga zaman lafiya a Janairu 2026.
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya ziyarci Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II da filin da za a yi Maulidin Darikar Tijjaniyya a Katsina.
Iyalan babban Shehin Darikar Tijjaniyya, Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya sun ce har yanzu ba su san a wane waje aka tsare mahaifinsu ba kwanaki 25 da kama shi.
Malaman darika
Samu kari