Yan bindiga
Rahotanni sun ce barkewar cutar kwalara ta kashe akalla yan bindiga shida, ciki har da mataimakin Muhammadu Gwaska, a maboyarsu da ke karamar hukumar Anka a Zamfara.
Iyalan Mai Shari'a Faruk Bunza sun tabbatar da biyan Naira miliyan 50 domin ceton sa daga hannun 'yan bindiga bayan kwanaki takwas yana tsare a Kebbi.
Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga sun nada sabon kwamanda bayan mutuwar Kachalla Iliya Mai Rasha, yayin da ake zargin an kakaba haraji kan kauyuka a Tsafe.
Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa 'yan bindiga aikin leƙen asiri bayan harin satar mutane a Alkaleri.
Bishop David Oyedepo ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi isasshen kokari wajen dakile kashe-kashe a Najeriya ba, yana mai cewa zai yi addu'a a kan masu aikata laifukan.
Yan bindiga sun kashe mutum 1 tare da sace mutane 31 a kauyen Shuwaki da ke karamar hukumar Bakori a Katsina, lamarin da ya kara tayar da hankalin mazauna yankin.
Wasu ‘yan bindiga sun sace dagacin Patiko da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja, tare da neman kudin fansa naira miliyan 80. Sun kira mutane waya.
Rahoto ya nuna cewa an sako alkalin Babbar Kotun Kebbi, Mai shari'a Faruku Hassan Bunza, bayan ya shafe mako guda a hannun masu garkuwa da mutane.
A labarin nan, za a ji cewa dakarun SSS da hadin gwiwar yan sa kai sun yi shiri bayan an samu labarin cewa yan dabar yan bindiga biyu sun kitsa kai hari Katsina.
Yan bindiga
Samu kari