Yan bindiga
Rundunar 'yan sandan Benue ta kama wani matashi mai shekara 20 da ake zargin yana kai wa 'yan bindiga alburusai bayan gano harsasai 115 masu rai a hannunsa a Guma.
Mazauna Kurudu sun bayyana yadda aka kashe Kanal Abdulrazaq Ude a babban birnin tarayya Abuja, yayin da surukinsa ya ce kisan shiri ne ba yunkurin garkuwa ba.
A labarin nan, za a ji cewa gwamantin Oyo ta fara nemo dalilin da yan bindiga su ka samu damar kutsawa har cikin jihar aka sace dalibai da malamansu.
Masu amfani da shafin X sun yi alhinin rasuwar Kanal Abdulsalam Ude, suna yabonsa a matsayin malamin Alkur'ani kuma gogaggen jami'in leken asiri.
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ga ‘yan ta’adda ba, tare da bayyana shirye-shiryen kara rundunonin soji da kafa ‘yan sandan jihohi.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai takwas na Gateway ICT Polytechnic a Ogun, yayin da mahukuntan makarantar suka soke wasu jarabawa saboda lamarin.
Iyalin mutum 176 da ‘yan ta’adda suka sace a Kaiama ta jihar Kwara sun roƙi gwamnati ta ceto su, bayan sun shafe kusan watanni shida a hannun masu garkuwa.
Wani alƙalin kotun Shari'a a jihar Katsina ya tsere ta taga bayan 'yan bindiga sun kai hari kotu suna neman shi, lamarin da ya sake tayar da hankalin mazauna yankin.
DSS tare da jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga uku, sun ceto mutum tara da aka sace a dajin Kwara bayan musayar wuta mai zafi da masu garkuwar.
Yan bindiga
Samu kari