Yan bindiga
'Yan bindigan da suka sace mutanen da ke yin ibada a coci a jihar Kaduna, sun bukaci a ba su kudaden fansa. 'Yan bindigan sun jero sharuddan da suke so a cika musu.
Kakakin jam'iyyar APC a jihar Zamfara ya bayyana cewa katin Bello Turji na jam'iyyar na bogi ne. Yusuf Idris ya ce Bello Turji ba dan jam'iyyar APC ba ne.
Rundunar 'yan sanda a jihar Gombe sun sanar da cewa an gwabza fada da 'yan bindiga a wani yanki na Pindiga a karamar hukumar Akko. An kashe mutum 3.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun sace yan kasuwar ne a lokacin da suka dawo daga sayayya a kasuwar Moro, karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina. Tsagerun 'yan bindigan sun kashe jami'an tsaro na 'yan sa-kai a wani artabu.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Katsina. Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Amarya da kawayenta a Sokoto sun sami 'yanci bayan kwanaki 49 a hannu 'yan bindiga, bayan biyan fansa Naira miliyan 10, lamarin da ya jefa al'umma cikin tsoro.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wasu mutane da ke hakar ma'adanai a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun yi kisan kai yayin harin da suka kai.
Bayan harin yan bindiga a Kaduna, kasar Amurka ta buƙaci Najeriya ta ƙara tsaurara matakan kare Kiristoci bayan sace-sace a coci da aka yi a jihar.
Yan bindiga
Samu kari