Yan bindiga
Malamin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tura sako ga Bello Turji da sauran yan ta'adda bayan kisan Halilu Sabubu da safiyar ranar Juma'a.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin 'yan bindigan da suka kashe Sarkin Gobir. Sojojin sun sheke uku daga cikin miyagun har lahira.
Hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ya ba da kyautar kudi ga dakarun sojoji da suka yi nasarar hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu a Zamfara a jiya Juma'a.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba kan nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan 'yan bindiga. Ya yaba kan kisan da aka yiwa Halilu Buzu Sububu.
Kwanaki uku kafin hallaka rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu, an wallafa faifan bidiyo inda ya ke rokon yan uwansa kan lamarin tsaro ciki har da Bello Turji.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa akwai makarkashiya a lamarin tsaron jihar kowa ya sani kuma wasu ne manya a sama da ke siyasantar da shi domin bukatunsu.
Gwamnan jihar Katsina ya sake shirin fuskantar yan ta'adda irinsu Bello Turji wajen daukar yan sa kai. An ware kudi N1.5bn domin daukar yan sa kai a Katsina.
A yayin da jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin PDP mai mulki a Zamfara da gaza kawo karshen ta'addanci, ita ma gwamnatin jihar ta yiwa APC zazzafan martani.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-hare a jihar Zamfara da safiyar ranar Alhamis. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an sojoji uku bayan sun bude musu wuta.
Yan bindiga
Samu kari