Yan bindiga
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai hari a jihar Imo. Jami'an tsaro na sojoji sun fito sun fafata da su lamarin da ya jawo asarar rayuka tare da raunata wasu mutane.
'Yan bindigan da suka sace Hakimin Kanya a jihar Kebbi sun yi sanadiyyar rasuwarsa bayan sun ji masa rauni a kai. Jami'an tsaro sun ceto mutum takwas.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun salwantar da rayukan mutane biyar bayan sun kai wani hari a jihar Anambra. 'Yan bindigan sun bude wuta kan bayin Allah.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alhinin kisan da 'yan bindiga suka yi wa jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara a wani harin kwanton bauna.
Yan bindiga sun kai hari kan askarawa masu bayar da tsaro a yankin Tsafe inda suka kashe mutane 8. Yan bindigar sun yi kwanton bauna ne ga askarawan da safe.
Yan sanda sun yi musayar wuta da yan bindiga a kananan hukumomin Katsina kuma sun ceto mata da yara kanana daga kamun masu garkuwa bayan tafka kazamin fada.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da daukar yan sa kai 500 domin cigaba da yakar yan bindiga a Katsina. Dikko Radda ya ce za a cigaba da yakar yan bindiga.
Yan daba sun cinna wuta a kananan hukumomi biyu a jihar Rivers bayan zaben kananan hukumomi a jihar. Sun yi fashe fashe a wata karamar hukumar domin adawa da zabe.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga a jihar Kaduna. Jami'an tsaron sun sheke 'yan bindiga uku tare da ceto wasu mutane.
Yan bindiga
Samu kari