
Jos







Mashawarcin shugaban kasa, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa dole ne a samu hadin kan jama'a idan har za a yaki matsalar rashin tsaro da gaske a jihar Filato.

Babbar kotu da ke zamanta a Jos din jihar Plateau ta dage shari’ar kisan gilla kan Manjo-Janar Idris Alkali zuwa 28 da 29 ga watan Mayun shekarar 2025.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga munanan hare-haren da yan bindiga suka kai a yankin Bokkos sun ba da labarin yadda lamarin ya faru ba zato ba tsammani.

Wata gagarumar iska da ta biyo bayan mamakon ruwan sama a jihar Filato ta rigurguza gidaje da rumbunan abinci sama da 70 a karamar hukumar Langtang ta Kudu.

Bayan rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhinin rasuwar Abdullahi Shuaibu da aka fi sani da Karkuzu a Jos.

Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang ya kulla yarjejeniya da Isra'ila kan aikin noma, fasaha da kiwon lafiya domin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Shugaban Izala mai hedkwata a Jos, jihar Filato, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yaba wa Gwamna Caleb Mutfwang bisa koƙarin da yake yi na inganta rayuwar al'umma.

Marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir ya taba musuluntar da kabilar Cakobo baki daya, dukkan mutanen kabilar da sarkinsu. Malamin ya fara karatu wajen mahaifinsa.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a Filato ta karyata cewa akwai kasuwar da ake sayar da sassan jikin dan Adama a jihar. An gargadi iyaye kan tarbiyya.
Jos
Samu kari