Zaben Shugaban kasan Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karasa kotu da wata daga cikin Masu ba Muhammadu Buhari shawara, ya yi karar ta da laifin ci masa mutunci.
Buba Galadima ya fadi yadda aka yaudari mutane da addini da tikitin Musulmi da Musulmi. Jagoran NNPP yace babu wanda ya san halin ‘dan siyasa kamar abokinsa.
Mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar a 2019, Segun Showunmi ya nuna zai dauki mataki domin ba zai juri yadda abubuwa suke cigaba da tafiya a PDP ba.
Wole Soyinka yana zargin an shirya makarkashiya tun farko kafin zaben domin a tabbatar da cewa ba ayi zabe ba. Farfesan ya ce saura kiris tarihi ya maimaita kan shi.
Na kusa da Goodluck Jonathan ya fadi wanda zai hana PDP lashe zabe a 2027. Reno Omokri ya ce idan Peter Obi bai tsaya takara ba, Atiku Abubakar zai iya nasara.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi magana kan yiwuwar kwace mulkin kasar nan daga hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2027.
Wasu 'yan adawa sun fara amsa kiran Atiku Abubakar na hada-kai domin a karbe mulki. Watakila ayi taron dangi da nufin ganin bayan Bola Tinubu a zaben 2027.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya fadi yadda aminan Bola Tinubu su kayi sanadiyyar zamansa Shugaban kasa bayan lashe zaben 2023.
Daniel Bwala, kakakin rushashiyar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar zai sake takara a 2027.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari