Zaben Shugaban kasan Najeriya
Mun kawo jerin ‘yan siyasan da su ka fi kowa yin asara a bana. Sun shiga takara ko aka sa ran za su samu mukami a gwamnati, amma sun tashi babu komai a 2023.
Ahmad Yariman Bakura za su kaddamar da kungiyar da za ta goyi bayan tazarcen Bola Tinubu a 2027. Domin ganin APC ta cigaba da mulki, ‘yan siyasan sun fara shiri.
Takarar Atiku Abubakar a zabe mai zuwa ta na cikin hadari. Bode George ya ce a zaben 2027, babu wanda zai nemi tikitin jam’iyyar PDP sai mutanen yankin kudu.
Salihu Lukman ya ce shaharar Bola Ahmed Tinubu a siyasa ta taimaka ya zama ‘dan takaran APC a zaben 2023. Watanni da hawa mulki, jagoran na APC ya ce akwai gyara.
Babbar kotu a jihar Legas ta garkame jigon APC, Wahab Hammed kan zargin siyan kuri'u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara.
Peter Obi ya dauki lokaci mai tsawo yana ta sukar gwamnatin APC. Kashim Shettima ya fitar da jawabi cewa Peter Obi mayaudari ne, har yanzu yake haushin rasa zabe.
Kungiyar CAGRAM ta sha alwashin nemawa Shugaba Tinubu kuri'u a gabanin zaben 2027 da zai ba shi damar yin tazarce. Hakan ya biyo bayan ayyukan Tinubu a Najeriya.
Jam'iyyar HDP ta bayyana cewa kundin dokar Lis Pendens ya ayyana zaben shugaban kasar 2023 matsayin 'haramtacce' don haka Tinubu bai kamata ya zama shugaban kasa ba.
Dr. Muazu Babangida Aliyu ya ce siyasa sai mutanen banza, yake cewa tun daga wajen sayen fam zuwa zaben tsaida gwani, an yi waje da mutanen kirki daga samun mulki.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari