Zaben Shugaban kasan Najeriya
Tsohon shugaban PDP, uche Secondus ya ce APC na shirin kashe dimokuradiyya a Najeriya wanda hakan zai iya hana yin zabe a Najeriya a shekarar 2027.
A wannan labarin, za ku ji tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Felix Osakwe ya shawarci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ajiye mukamin Ministan man fetur.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar NNPP a zaben shugaban kasa na 2023 ya ce jam'iyyar za ta taka rawar gani a zaben 207 yayin da ta dauki matakai tun yanzu.
Shugaban kungiyar Concerned Nigerians, Kwamared Deji Adeyanju ya yi ikirarin cewa jami'an hukumar DSS sun cafke Omoyele Sowore a filin jirgin Legas.
Jam’iyyar PDP ta fallasa abubuwan da INEC ta yi a zabukan 2015 zuwa 2023. Umar Iliya Damagum ya zargi hukumar INEC da murde zabukan da aka yi a 2019 da 2023.
Tsohon mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya ce ƴan Najeriya za su buga Bola Tinubu da ƙasa a babban zaɓen 2027.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya shawarci Rabiu Musa Kwankwaso da ka da ya yi takara a zaben 2027 da ke tafe.
Jam'iyyar APC mai mulki ta barranta da maganar takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa. An hango alluna takarar shugaban kasar a Abuja
A wani sabon mataki da tsagin jam'iyyar Labour karkashin Julius Abure ya dauka, jam'iyyar ta fasa tanadarwa Peter Obi tikitin takarar shugaban kasa a 2027.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari