Zaben Najeriya
Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP sun yi taro a Enugu inda suka koka kan halin da Najeriya ke ciki na wahala. PDP ta bukaci a zabe ta a 2027 domin saukaka rayuwa.
Sanata Ifeanyi Ubah da wasu manyan kusoshin APC daga jihar Anambra sun gana a birnin tarayya Abuja, ana zargin sun fara shirin tunkarar babban zaɓen gwamna.
Hukuncin kotun ƙoli na ba kananan hukumomi ƴanci ya sa gwamnoni sun fara gaggawar shirya zaben kananan hukumomi a jihohinsu. Mun tattara maku su duka.
Tsagin NNPP ya zargi dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso da kokarin kwace jam'iyyar,lamarin da ya ce ba za su amince ba.
Yan Najeriya na tsaka da bayyana rashin gamsuwa da yadda Bola Tinubu ke mulkar kasar, sai ga shi an fara shirye-shiryen ya sake tsayawa takara a 2027.
Shugaban Malaman kungiyar Izala Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana cewa za su sake zaben tiketin Musulmi da Musulmi a zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Jam'iyyar NNPP ta kaddamar da sabon tambarin jam'iyya yayin da ta sha kaye a zaben 2023 da ya gabata bara. An bayyana dalilin sauya tambarin baktatan.
Jigon jam'iyyar APC a Kano, Dan Bilki Kwamanda ya yi martani kan kura-kuran da gwamnatin Bola Tinubu ke aikatawa a Najeriya inda ya ce zai samu matsala a zabe.
Kungiyar matasa masu goyon bayan Atiku, NYFA, ta ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai kawo sauyi ga al’ummar kasar idan ya zama shugaban kasa.
Zaben Najeriya
Samu kari