Zaben Najeriya
Jam'iyyar ADC mai adawa ta ce Atiku Abubakar ba zai janye daga takarar 2027 ba, yayin da Chille Igbawua ya yi watsi da sukar shekarunsa da lafiyarsa.
Hukumar INEC ta bukaci kotu ta yi watsi da karar Atiku Abubakar kan takardun shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda rashin iko ko hakkin shigar da korafin.
Abdul’aziz Yari ya bayyana cewa Allah ne ya zabe shi don jagorantar yakin zaben Bola Tinubu na 2027, sannan ya roki goyon bayan al'umar jihar Zamfara.
Matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ta bayyana cewa 'yan Najeriya za su samu tagomashi idan ya yi nasara.
Atiku Abubakar ya ce ADC za ta horar da matasa miliyan 1.5 domin kare ƙuri’un jam’iyyar a rumfunan zaɓe yayin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
INEC ta yi watsi da shirin Peter Obi na tattara sakamakon zabe ta wata hanya ta daban, yayin da ADC ta goyi bayansa, masana sun fadi fa’idodi da kalubalen tsarin.
Peter Obi ya ce ya lashe zaben 2023, yayin da APC da Fadar Shugaban Ƙasa suka yi watsi da ikirarinsa, suna cewa zai fuskanci rashin nasara a 2027.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar zabe ta INEC ta amince da sabon tambarin NDC mai alamar yatsu biyu tare da hana hukumar tsoma baki.
Peter Gregory Obi ya musanta rahotannin cewa ya ƙi zama mataimakin Atiku Abubakar a zaɓen 2027, yana mai cewa ba a taɓa miƙa masa irin wannan tayin ba.
Zaben Najeriya
Samu kari