Zaben Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a LP kuma tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa yana neman a ba shi mataimakin shugaban kasa a 2027.
Jam’iyyar PDP ta fallasa abubuwan da INEC ta yi a zabukan 2015 zuwa 2023. Umar Iliya Damagum ya zargi hukumar INEC da murde zabukan da aka yi a 2019 da 2023.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kano ta bayyana cewa an jirkita labarin 'yan takarar zaben kananan hukumomi mai zuwa.
A labarin nan, za ku ji cewa jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta barranta yan takararta a zaben kananan hukumomi mai zuwa da amfani da miyagun kwayoyi.
A wani sabon mataki da tsagin jam'iyyar Labour karkashin Julius Abure ya dauka, jam'iyyar ta fasa tanadarwa Peter Obi tikitin takarar shugaban kasa a 2027.
Wasu allunan da ke tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun fara bayyana a birnin tarayya Abuja. Ana tallata Tinubu ne domin zaben 2027 da ke tafe.
Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ya ba da tabbacin gudanar da sahihin zaben kananan hukumomi a jihar. Ya bukaci 'yan adawa su shiga zaben.
Jigon jam'iyyar NNPP kuma dan takararta zaben shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta musu murus gaba daya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya yabawa Kungiyar LND da Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta da aka kafa domin kawo sauyi a Najeriya.
Zaben Najeriya
Samu kari