Zaben Najeriya
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa sun fara tattaunawa da NNPP da PDP domin hada karfi su kifar da Bola Tinubu a 2027.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan ya bayyana cewa ya zama dole hukumar ta yi abubuwan da za ta samu yardar yan Najeriya musamman matasa.
Shugaban APC na jihar Kwara, Sunday Fagbemi ya bayyana cewa yawan gwamnoni zai taimaka wajen samun nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Kwanaki kaɗan bayan sauya shekar Peter Obi zuwa ADC, Datti Baba-Ahmed ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasar Najeriya a 2027 ƙarƙashin jam’iyyar LP,
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya nesanta kansa da yakin neman takarar gwamnan Neja a 2027 tare da dakatar da hadiminsa Sa’idu Enagi da ya yi rubutun.
A labarin nan, za a ji wani jigo a PDP, Emmanuel Ogidi,ya bayyana cewa lokaci kawai ake jira da Nyesom Ezenwo Wike zai yi wa APC abin da yi wa jam'iyyarsa.
Shugaban APC Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi alkawarin ƙuri'u miliyan 1 ga Tinubu a 2027 a Filato, bayan sauya shekar Gwamna Mutfwang zuwa jam'iyyar APC.
Dr Yunusa Tanko, na Obedient Movement, ya ce Peter Obi zai yi takara a 2027, yana tabbatar da alkawarin wa’adi daya da zai mayar da mulki ga Arewa.
Kungiyar dattawan Arewa, ACF ta bayyana cewa ba za ta goyi bayan kowane dan takarar shugaban kasa ba a 2027, amma za ta tattauna da su kan tsaro, talauci, da ilimi.
Zaben Najeriya
Samu kari