EFCC
A wannan rahoton, hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce a shirye ta ke wajen fuskantar tsohon gwamnan Kogi, Bello Yahaya a kotu.
Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci fara bincike kan zargin cin hanci a gidan yari bayan dan daudu, Bobrisky ya fasa kwai lokacin da ya ke can.
A wannan labarin, za ku ji babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage fara sauraren shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello zuwa watan gobe.
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana yadda ya taimakawa Dauda Lawal da muƙamin hadiminsa wurin samun fasfo da EFCC ta kwace masa lokacin mulkinsa.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar EFCC sun cika hannu da wasu mutane uku da ake zargin suna sayen kuri'u a yayin da ake gudanar da zaben jihar Edo.
Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyana cewa Yahaya Bello ya sake sulalewa a karo na biyu da taimakon gwamnan Kogi amma har yanzu ana nemansa ruwa a jallo.
Rahotannin da muke samu yanzu sun tabbatar da cewa mutane sun shiga firgici bayan jin karar harbe-harbe da ake zaton EFCC ke kokarin cafke Yahaya Bello.
Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah wadai da sake ware makudan kudi har N30bn na wasu ayyuka inda ta bukaci hukumar EFCC ta fara bincike a kai.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya baro babban ofishin hukumar EFCC ta ƙasa da ke Abuja, ya ce jami'ai sun amince ya tafi ba tare da sun masa tambayoyi ba.
EFCC
Samu kari