
EFCC







Shugaba hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukoyede, ya bayyana nasarorin da hukumar ta samu a shekarar 2024 da ta gabata.

EFCC ta gurfanar da wasu mutum hudu a Kaduna bisa damfara da satar N197,750,000. Kotun ta bada umarnin tsare su, tare da dage sauraron belinsu zuwa Maris 17.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa ta sanya N50bn da kwato a hannun barayin gwamnati da masu zamba a asusun NELFUND.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa ta kwato kudade mafi yawa a shekarar 2024 daga hannun barayin da suka sace kudin gwamnati.

Bayan kama tsohon gwamnan Akwa Ibom, Gwamnan jihar, Umo Eno, ya nesanta gwamnatinsa daga zargin rashawa na ₦700bn da EFCC ke yi wa Udom Emmanuel.

Tsohuwar Ministar harkokin mata, Uju Kennedy Ohanenye ta na fuskantar tuhuma a kan kartatar da kudade, saba dokar sayo kayayyak i da almundahanar kudade.

Watanni biyar bayan dakatar da ita, hukumar EFCC tana bincikar tsohuwar ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, kan zargin karkatar da kudade har N138m.

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Kaduna ta sahale wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kwato wasu kudi da ake zargin an boye a lokacin Nasir El-Rufa'i.

Wani rahoto ya bankado yadda manyan jami'an gwamnatin Amurka, daga ciki har da tsohon shugaban kasar, Joe Biden su ka taimaka wa Shugaban Binance a Najeriya.
EFCC
Samu kari