Jihar Edo
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya ce dole a dauki mataki kan kisan 'yan Arewa da aka yi a Uromi na jihar Edo. Gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin biyan diyya kan Hausawan da aka kashe a Edo. Abba Kabir ya ce ya yi waya da gwamnan Edo kan lamarin.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da shugaban rundunar tsaron jihar kan mummunan kisan gillar da aka yi wa mafarauta 'yan Arewa a jihar.
Bayan kisan ƴan Arewa a jihar Edo, babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta.
Sarkin Kano, Mai Martaba, Muhammadu Sanusi II, ya yi Allah wadai da kisan 'yan Arewa da aka yi a jihar Edo, yana mai kira ga hukuma ta bi musu hakki.
Bayan kisan wasu ƴan Arewa fiye da 16 a Uromi da ke jihar Edo, a yau Asabar 29 ga watan Maris aka birne wasu daga cikinsu bayan samun gawarwakinsu.
Bayan Peter Obi ya jajanta kan kisan wasu ƴan Arewa a Edo, an taso shi a gaba kan yadda ya yi jajen tare da neman a hukunta masu kisan ƴan jihar.
Ministar al'adun Najeriya Hannatu Musa Musawa ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Hausawa 'yan Arewa a jihar Edo. An kashe mutanen ne suna dawowa Arewa.
Kungiyar sanatocin Arewa karkashin Sanata Abdul'aziz Yar'adua ta yi Allah wadai da mummunan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo, sun nemi adalci.
Jihar Edo
Samu kari