Zaben Edo
Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole da mataimakin gwamna Philip Shaibu sun lallasa jam'iyyar PDP bayan INEC ta fadi sakamakon zaben karamar hukumarsu.
Rahotanni sun bayyana cewa Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP Asue Ighodalo ya yi nasara a karamar hukumarsa ta Esan ta Kudu maso Gabas.
Nan da 'yan awanni za a san wanene zai zama sabon gwamna a jihar Edo inda ake zabe. INEC ta yi maganar soma tattara sakamako, a san wanda ya lashe zaben Edo.
Rahotanni daga cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke da zama a birnin Benin ta sanar da cewa PDP ta samu kuri'u 5,311 a Ovia ta Arewa maso Gabas.
Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Edo ta samu nasarar lashe karamar hukumar Uhunmwonde da kuri'u 9339 bayan da hukumar INEC ta ci gaba da sanar da sakamako.
Rahotanni daga cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke Benin City na nuni da cewa jam'iyyar APC ta lashe zabe a karamar hukumar Esan ta Yamma.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar PDP ta fara samun nasara a zaben gwamnan jihar Edo yayin da hukumar INEC ta fara tattara sakamakon zaben na jiya.
Hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan yadda wasu yan siyasa suka cika ofishinta a jihar Edo musamman bayan Gwamna Godwin Obaseki ya dira a ofishin da tsakar dare.
Zaben Edo
Samu kari