Zaben Edo
A ranar Asabar da ta wuce ne aka yi zaɓen gwamna a jihar Edo kuma APC ta samu nasara, sai dai aka ganin rikicin Obaseki da wasu ƙusoshi 5 ne ya kada PDP.
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ce an yi kwacen mulki a zaben Edo na 2024 kuma ya bukaci a tafi kotu. Obaseki ya ce an tafka kurakurai a zaben.
Rundunar 'yan sanda ta tura karin jami'anta zuwa cibiyoyin INEC, manyan kadarorin gwamnati da 'yan siyasa domin dakile duk wata barazanar tsaro bayan zaben Edo.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce nasarar APC a zaben Edo ya nuna akwai alamar talakawa sun amince da salon mulkin Bola Tinubu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murna bayan APC ta lashe zaben gwamna a jihar Edo. Buhari ya bukaci yan takaran PDP da APC su hada kai domin cigaba a Edo.
Dan takarar jam'iyyar APC, Monday Okpebholo ya samu nasarar cin zabe a kananan hukumomi 11 cikin 18 a zaben jihar Edo da aka gudanar tare da samun kuri'u 291,667.
A ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba ne hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben jihar Edo daga kananan hukumomi 18. Jam'iyyar PDP ta lashe zabe a 7 cikin 18.
Bayan shafe awanni ana tattara sakamakon zaben jihar Edo, Hukumar zabe ta INEC bayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.
Yayin da ake dakon sakamakon zaben jihar Edo, Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun tura sako ga hukumar zabe ta INEC game da yin adalci a zaben.
Zaben Edo
Samu kari