Matsin tattalin arziki
Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin BUA ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta kai ₦1,300-₦1,400 kafin ƙarshen 2025, kuma farashin abinci zai kara sauka.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa karin kudin shiga ba zai hana karbo bashi ba. Shugaban hukumar FIRS Zacch Adedeji ya ce Najeriya za ta cigaba da ciwo bashi.
Ministan kudi, Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta maida shirin tallafin ragw radadi ya zama a na kowace shekara, ya ce mutane da dama sun amfana.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan hanyar bunkasa tattalin arziki da bukatar ƙasashe su haɗa kai wajen yakar yunwa da bunƙasa noma.
Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ne ta lalata tattalin Najeriya, Tinubu kuma yana gyara shi.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin dakile talauci gaba daya a fadin Najeriya inda ta ce za ta bi duk hanyar da ta dace domin kawo sauyi a kasa.
Fadar shugaban kasa ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na dab da sauka zuwa kasa sosai inda ta ba da tabbacin hakan saboda matakan da ake dauka.
Darajar Naira ta karu, inda ake yin cinikinta ƙasa da N1,500 kan kowace Dala, a karon farko cikin watanni takwas, sakamakon sababbin dabarun tattalin arziki.
Hukumar NBS ta futar da alkaluman farashin kayayyaki a Najeriya, ta tabbatar da cewa jama'a sun jara samun sauki a farashin kayan abinci a watan Agusta, 2025.
Matsin tattalin arziki
Samu kari