Matsin tattalin arziki
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya bayyana cewa wutar lantarkin jihar Bayelsa ta lalace tun watanni 3 da suka shige har yau jama'a na rayuwa a duhu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nuna damuwa kan yadda tsadar rayuwa ta dabaibaye Najeriya inda ya shawarci Bola Tinubu kan lamarin.
Sanata Ali Ndume ya samu kariya bayan an fara maganar masa kiraye kan sukar kudirin haraji ba Bola Tinubu. Mutanen Borno suna goyon bayan Ali Ndume.
Gwamnatin jihar Katsina ta kafa tashoshin mota domin rage radadin tsadar rayuwa da cire tallafin man fetur. An bude tashoshin mota a Mashi da Ingawa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yaba kan yadda 'yan Najeriya suka nuna juriya kan halin matsin tattalin arziki da aka shiga sakamakon tsare-tsaren da ta fito da su.
Binciken Majalisar Dinkin Duniya, shirin samar da abinci na duniya, ma’aikatar noma da samar da abinci ta Najeriya ya gano miliyoyin da za su kamu da yunwa a 2025.
Sanata Bala Mohammed ya kafa kwamitin karya farashin abinci a jihar Bauchi. Kwamitin zai rika sayen abinci har na N3bn domin sayarwa talakawa da araha.
Yan kasar nan sun ce wahala ta ishe su, saboda haka su ka garzaya majalisar tarayyar Najeriya su na neman daukin mahukunta kan a sake duba bangaren fetur.
Kungiyar abinci da harkokin noma ta majalisar dinkin duniya ta bayyana abubuwan da take ganin sun hefa ƴan Najeriya cikin damuwa da kuma mafita a kansu.
Matsin tattalin arziki
Samu kari