Matsin tattalin arziki
Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi martani mai zafi ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan maganganun da ya yi ranar Lahadi kan matasa masu zanga zanga.
Tun bayan jawabin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ga 'yan kasar nan aka samu masu ganin rashin ingancin jawabin saboda kin duba koken 'yan kasa.
Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama Michael Lenin, daya daga cikin jagororin zanga-zangar 'kawo karshen mummunan mulki' da ake yi a birnin Abuja.
Bayan fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Kano, an zargi yan sanda da kashe masu zanga zanga a Kurna da Nasarawa kamar yadda Jafar Jafar ya wallafa.
Wanda ya lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce Shugaba Bola Tinubu bai yi magana kan ta’asar da ‘yan sanda ke yiwa masu zanga-zangar yunwa a kasar nan ba.
Tsohuwar shugabar hukumar raya Neja Delta (NDDC), Ibim Semenitari ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya magance tsadar abinci domin talaka na shan wuya.
Masu zanga-zangar, wadanda suka fara a ranar Lahadi, 1 ga Agusta a Ring Road da ke Benin da kewaye, sun dakatar da zanga-zangar bayan jawabin Shugaba Tinubu.
Jagororin matasa sun sanar da janye zanga-zangar da suke yi a yankin Ojota da ke jihar Legas bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da jawabi a safiyar Lahadi.
Wasu matasa sun tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Ojota da ke jihar Lagos da cewa ai Shugaba Bola Tinubu ya riga ya yi jawabi ga 'yan kasar kan matsalar.
Matsin tattalin arziki
Samu kari