Matsin tattalin arziki
Bankunan Najeriya sun kara cajin kudin tura sakon kudi daga N4 zuwa N6 daga yau Alhamis 1 ga Mayu. Sun yi karin ne saboda karin kudin sadarwa da aka yi a Najeriya.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya ce talauci ba laifi ba ne, yana kiran ‘yan Najeriya da su rungumi juna da raba abin da suka mallaka.
Farashin buhun shinkafa ya sauka zuwa N58,000 a Najeriya sakamakon shigo da shinkafar Indiya ta barauniyar hanya daga Jamhuriyar Benin zuwa kasuwannin kasar nan.
Sanata Olamilekan Adeola ya yabawa Bola Tinubu kan kokari a fannin tallalin arziki bayan Muhammadu Buhari ya aro $400bn don daidaita darajar naira.
Bankin duniya ya fitar da rahoto kan yadda talauci zai yi wa 'yan Najeriya katutu zuwa 2027. Bankin duniya ya ce 'yan Najeriya da dama za su kara talaucewa.
Fasto Tunde Bakare ya shawarci Shugaba Tinubu ya rungumi tawali’u da karɓar shawara domin ceto Najeriya daga halin da take ciki inda ya ce an gaji da addu'a.
Hukumar kididdiga ta ƙasa watau NBS ta bayyana cewa an samu ƙarin hauhawar farashin kayayyaki daga 23.18% a watan Fabrairu zuwa 24.23% a watan Maris, 2025.
China ta kara haraji kan kayayyakin Amurka zuwa 125% yayin da rikicin kasuwanci ya kara kamari. China ta ce ta shirya yin karar Amurka gaban hukumar WTO.
A kasuwar hatsi ta Potiskum da ke jihar Yobe, wake ya yi tashin gwauron zabi yayin da farashin masara, dawa da gero suka sauka. Ana sayar da shinkafa kan N51,000.
Matsin tattalin arziki
Samu kari