Matsin tattalin arziki
Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan halin kunci da 'yan kasar ke ciki wanda ya tilasta zanga-zanga a birane da dama.
Masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun koka bisa yadda jami'an tsaro su ka kashe wasu daga cikinsu a sassan kasar a lokutan da su ke tattaki.
Ministan kudi, Wale Edun ya yi magana kan batun dawo da tallafin mai inda ya ce kwata-kwata babu tsarin a kasafin kudin wannan shekara ta 2024 da ake ciki.
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da kama wasu ‘yan kasashen waje da ke daukar nauyin masu zanga-zanga suna daga tutar kasar Rasha a Kano. Bayanai sun fito.
Majalisar Matasan Arewa ya yi tir da bukatar da wasu mutane ke yi na gwamnati ta sauyawa cibiyar fasaha ta hukumar sadarwa matsuguni zuwa jihar Kebbi.
An ce wa'adin biyan wani bashi da Dangote ya karba zai cika karshen watan Agusta, saboda hakan ya fara shirin sayar da 12.75% na hannun jarin matatarsa.
Gwamnatin tarayya ta yi martani ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar bayan shawartar jami'an tsaro da su dai na harbin masu gudanar da zanga-zanga.
Kimanin 'yan siyasa 4 na Arewa ne jami'an tsaro suka fara tuhuma kan zargin daukar nauyin daga tutocin kasar Rasha a lokacin zanga-zangar yunwa da ake yi.
Shugaban hukumar kwastam na ƙasa, Bashir Adeniyi ya ce ana sa ran za a samu saukar farashin kayayyaki a nan ba da jimawa ba yayin da aka dakatar da haraji.
Matsin tattalin arziki
Samu kari