Matsin tattalin arziki
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan zanga-zanga a Kano inda ya ce ya samu bayanan sirri Gwamna Abba Kabir ne ya dauki nauyin zanga-zangar.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya sanar da shirinsa na fara sayar da shimkafa a farashi mai rangwamen kaso 51%, ya ce hakan zai ragewa mutane raɗadi.
Dattijon kasa, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa ba kundin tsarin mulkin Najeriya ce ke da matsala ba, kar a bar jaki ana dukan taiki, ya ce a sauya tunani.
Kamfanin simintin Dahiru Mangal ya ƙaryata jita-jitar siyar da buhu kan farashin N6,000 kamar yadda ake yaɗawa a kafofin sadarwa inda ya ba al'umma shawara.
Matasan APC sun ga rashin dacewar zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu na kwanaki 10, inda ta shirya tattakin goyon bayan shugaban kasa.
Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin bullo da sababbin shirye-shiryen tallafi domin magamce wahalhalun tsadar rayuwar da mutane ke fama da su a jihar.
Bayan kammala zanga-zangar adawa da.manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, 'yan Najeriya ba su samu saukin da su ka yi fata ba, domin kayan masarufi na hauhawa.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya dauki matakin hana hadimansa na siyasa fita wajen jihar idan gwamnati ce za ta dauki nauyinsa duba da tattalin arziki.
Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus Adejugbe ya haramta kungiyoyin 'yan kasuwa da ke tsauwalawa mutane kan tsadar kaya tare da kayyade farashin kayan abinci.
Matsin tattalin arziki
Samu kari