Matsin tattalin arziki
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sake sako gwamnatin Tinubu a gaba kan manufofin da ya ce su na kashe yan Najeriya da jefa su a wahala.
Shafi’u Umar Tureta, tsohon hadimin gwamnan Sakkwato ya bayyana yadda ya tarar da mazauna gidan yari bayan laifin da ya yi yi wa gwamnan jiharsa ya kai shi zama can.
Sarakunan gargajiya sun hada kai sun tunkari gwamnatin tarayya kan tsadar rayuwa. Sarakuna sun bukaci Bola Tinubu ya saukakawa talakawan Najeriya.
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya shawarci gwamnatoci su dauki matakin shawo kan matsalolin Najeriya kafin juyewa zuwa wani abin daban duba da halin kunci.
Rundunar yan sandan Najeriya ta kara musanta cewa jami'anta sun kama yara masu kananun shekaru yayin zanga zangar adawa da manufofin gwamnatin Tinubu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ana kan hanyar fita daga wahalar rayuwa duk da ana shan wahala a yanzu. Tinubu ya ce sai an dauki lokaci kafin samun gyara.
Sanatan Neja ta Gabas, Mohammed Sani Musa ya ce ba a fahimci abin da yake nufi ba kan cire tallafin mai, ya ce wasu mutane kalilan ke cinye kudin da ake warewa.
Kungiyar kwadago ta ce yunwa ta fara haifar da cututtuka kama su kwashoko a Najeriya. NLC ya ce akwai bukatar fitar da tare tsaren kawo saukin rayuwa.
Sanata mai wakiltar Jigawa shiyyar Arewa ta Yamma, Babangida Hussaini ya bayyana irin matsalar da jama'ar kasa ke ciki na yunwa da matsin rayuwa.
Matsin tattalin arziki
Samu kari