Hukumar EFCC
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta dage shari'ar da ake yi tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam.
Hukumar Yaki da Masu Yi wa tattalin arzikin kasa ta'adi watau EFCC ta cafke wata malamar coci, Archbishop Angel Oyeghe bisa zargin cin zarafin Naira.
A labarin nan, za a ji yadda kungiyar SERAP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso a kan ya yi bayani a kan bacewar N3trn daga bankin.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta bayyana neman tsohon gwamna Timipre Sylva saboda zargin karkatar da kuɗin gina wata matatar mai.
EFCC ta ayyana tsohon ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dala miliyan 14.8.
EFCC ta mayar wa wata tsohuwa mai shekara 70, Margret Taye Odofin, N42.5m da jami’ar banki ta sace mata, bayan shekara da dama tana neman adalci.
Jami’an EFCC sun isa Anambra yayin da ake gudanar da zaben gwamna don tabbatar da cewa babu sayen kuri’a, inda aka ga jami’an jam’iyyun siyasa suna karbar katin zabe
Rundunar ‘Yan sanda ta janye karar Naira miliyan 400 da ta shigar kan tsohon Sanata Andy Uba da abokinsa, bayan sulhu tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
Wasu rahotanni sun ce hukumar EFCC da NFIU sun fara bincike kan yadda aka so amfani da wasu kudi a shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hukumar EFCC
Samu kari