Daukan aiki
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nada manyan sakatarori biyar a ma'aikatar gwamnatin tarayya. Wadanda aka nada sun fito daga yankunan kasar.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Tunji Ojo ya ba da umarnin gyara shafin daukar aikim hukumomin da ke karkashin CDCFIB, kuma ga dukkan alamu an aamu ci gaba.
Hukumar CDCFIB ta saki sunayen masu neman aiki a hukumomi hudu; NIS, FFS NSCDC da NCoS domin zuwa mataki na gaba idan sun yi nasara a matakin farko.
Alhaji Aliko Dangote ya tura ma'akatan da ya kora zuwa jihohin Zamfara, Borno Benue bayan dawo da su bakin aiki. An kori ma'aikatan ne bayan rikici da PENGASSAN.
Tsohon Ministan Harkokin Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa fasahar zamani kamar AI ba za su kwace ayyyukan mutane ba sai dai su karo dama.
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin samar da ayyukan yi a fadin dukkan jihohi. Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeochace ta bayyana haka a Legas.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bude shafin fara daukar sababbin ma’aikata 3,000 a dukkan kananan hukumomi 23 daga 22 ga Satumba 2025 zuwa 6 ga Oktoba, 2025.
A labarin nan, za a ji cewa tsofaffin ma'aikatan kasar nan sun fara baranzar fara zanga-zanga tsirara saboda mawuyacin halin da su ke ciki a yanzu.
Akalla gwamnoni uku a Najeriya ne suka kori ma’aikata a watan Satumba: Otti a Abia, Bala a Bauchi, Aiyedatiwa a Ondo, bisa laifuffukan rashawa da cin zarafi.
Daukan aiki
Samu kari