Dollar zuwa Naira
Babban Bankin Najeriya, CBN ya biya bashin Dala $7bn na daloli da tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele ya ciyo lokacin da ya ke rike da kujerar gwamnan bankin.
Ahmed Adamu wanda shi Farfesan da ke ba Atiku Abubakar shawara a kan sha'anin matasa ya fadawa Tinubu da CBN sirrin dawo da Dala $1 ta koma N200 a yau.
Tsakanin Talata da Laraba, Naira ta fadi da N12.56, bayan an yi hada-hadarta kan Dala a N1,603.38/$1 zuwa N1,615.94/$1, ana fargabar faduwar zai haifar da tsada.
Bankin CBN ya yi nasarar sayar da wasu takardun kudin baitul-mali na Naira tiriliyan 1.3 ga masu zuba jari na kasashen waje (FPI) a ranar Laraba, 6 ga Maris, 2024.
Gwamnatin Najeriya ta ci Binance tarar $10b bayan kama kamfanin da aika laifukan da taimaka wajen faduwar darajar Naira tare da jawowa kasar asara mai yawa.
Babban kamfanin sarrafa kayayyakin abinci, Nestle Nigeria ya tafka asarar naira biliyan 104.03 bayan da darajar Naira ta fadi a kasuwar duniya a 2023.
An tsare wasu manyan jami'ai biyu na kamfanin Binance a Najeriya, a cewar Financial Times (FT), wata kafar yada labaran kasuwanci da ke Birtaniya.
Babban lauya a Najeriya, Mike Ozekhome, ya yi hasashen cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, darajar Naira sai ta fadi kasa zuwa N4000/$1 kafin karshen 2024.
Bayan koken koken jama'a, an ji labari CBN ya cigaba da saida Daloli ga ‘yan kasuwar canji. Idan Dala ta fara wadatuwa a bayan fage, farashin Naira zai tashi.
Dollar zuwa Naira
Samu kari