Kasar waje
Ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu ya ce Najeriya ta fara fitar da kayan sola da ta kare zuwa kasuwannin Afrika ta Yamma. Ya ce an fara fitar da su Ghana.
Rundunar sojojin ruwa ta kasar Amurka ta tabbatar da hatsarin jiragenta biyu a tekun kudancin China, ta ce babu wanda ya rasa rayuwarsa a hadurran biyu.
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ya zarge ta da kera makamin nukiliya.
An sanar da rasuwar matar tsohon shugaban kasar Ghana, Nana Konadu Rawlings wacce ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 79 a duniya bayan fama da jinya.
Wata kotu a Ingila ta daure dan Najeriya na watanni 16 a gida yari kan amfani da sunan mace wajen yin aiki a wani asibiti, ta kuma ci tarar mutumin makudan kudi
Gwamnatin Kamaru ta sanar da cewa za ta gurfanar da matasa akalla 20 da aka kama a kotun soja kan zanga zangar bayan zaben shugaban kasa saboda tayar da tarzoma.
Malamin addinin Musulunci a kasar Habasha, Mufti Haji Umer Idris ya rasu yana da shekara 90 a duniya. Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwarsa.
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya shiga gidan yari bayan an kama shi da laifin karbar kudin kamfen daga Gaddafi, amma ya ce gaskiya za ta bayyana.
Fitaccen jarumin Bollywood, Asrani, ya rasu yana da shekara 84 bayan fama da matsalar numfashi. An fi saninsa da rawarsa ta “fursna” a fim din Sholay.
Kasar waje
Samu kari