Kasar waje
Yan majalisar dokonin jamhuriyar Benin sun tsawaita wa'adin shugaban kasa zuwa shekaru bakwai, sun ce babu wanda zai wuce wa'adi biyu a kan gadon mulki.
Hukumomin Najeriya sun ki mika Issa Tchiroma Bakary da ya buga takara da Paul Biya a zaben Kamaru. Kamaru na neman kama Bakary bayan zaben shugaban kasa.
Gwamnatin Kano ta tura dalibai 350 zuwa kasar India karatu. Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya bukaci su zama wakilai na gari yayin karatunsu a kasar waje.
Mutane shida sun mutu a wajen cunkoson daukar aikin sojoji a Accra, Ghana. Gwamnati ta dakatar da shirin kuma Shugaba Mahama ya ziyarci wadanda suka ji rauni.
Gwamnatin kasar Turkiyya ta tabbatar da mutuwar duka sojoji 20 da ke cikin jirgin C-130 da ya yi hatsari a kasar Georgia kusa da iyakar Azerbaijan.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon shugaban ƙasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya shaki iskar 'yanci bayan ya shafe makonni uku kacal daga cikindaurin shekaru biyar.
Gwamnatin tarayya ta tura tawaga zuwa kasar Birtaniya domin duba yiwuwar maido da Sanata Oke Ekweremadu gida Najeriya ya karisa zaman gidan yarinsa.
Majalisar Isra'ila ta karanta kudirin dokar da zai ba kasar dama hukuncin kisa ga Falasdinawa. Ana son kawo dokar da za ta hana kafafen yada labaran waje aiki.
Ofishin harkokin waje na gwamnatin Birtaniya (FCDO) ya sake fitar da sabon gargadi ga ‘yan ƙasar da ke shirin zuwa Najeriya. Ya ce su kauracewa jihohi 6.
Kasar waje
Samu kari