Kasar waje
Tsohon Firayim Ministan Biritaniya, Boris Johnson, ya ce ya ji cikakkiyar tsaro a Owerri duk da rahotannin tsaro da suka gabace shi kafin zuwansa Imo.
Wasu yan sa kai a Katsina sun kai harin kuskure kan sojojin Nijar da suka shiga Mazanya don ɗibar ruwa, lamarin da ya jawo damuwa har hedikwatar tsaro ta shiga ciki.
Daya daga cikin jagororin 'yan adawa a kasar Kamaru, Anicent Ekane ya rasu a hannun sojoji kwanaki bayan Paul Biya ya kama shi saboda wasu zarge-zarge.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gana da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa kan rikicin siyasar da ta barke bayan juyin mulki a Guinea-Bissau.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce ya ce juyin mulkin Guinea Bissau ya fi masa zafi a kan kayar da shi zabe da Buhari ya yi a 2015.
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bar Guinea-Bissau lafiya bayan rikicin siyasa, inda Ma’aikatar Harkokin Waje ta tabbatar da cewa babu wata matsala.
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin Najeriya ta bi duk hanyar da ta dace wajem dawo da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan daga Guinea-Bissau.
Gwamnatin Najeriya ta la’anci juyin mulkin soja a Guinea-Bissau, tana cewa matakin ya barazana ga dimokuraɗiyya, tsaro da kwanciyar hankali a yanki baki ɗaya.
Shugaban Amurka Donald J. Trump ya yi magana bayan wani dan bindiga ya harbi sojojin Amurka a kusa da fadar White House. Ya ce barazana ne ga tsaron Amurka.
Kasar waje
Samu kari