Kasar waje
Sojojin Isra'ila sun kakkabo makami mai linzami da aka harbo daga Yemen a yau, yayin da hare-haren Iran suka jikkata mutane a Kudus da sauran birane yau.
Yayin da ake ci gaba da musayar wuta a Gabas ta Tsakiya, Jamus ta roki China ta yi amfani da tasirinta ta lallaba Iran domin a kawo karshen wannan rikicin.
Hedkwatar rundunar sojojin Iran ta umarci manyan hafsoshi su kara sa ido kan yiwuwar shigar da dakarun makiya cikin kasar bayan barazanar Shugaba Donald Trump.
Kasashen da musulmi suka fi rinjaye ciki har da Saudiyya da Masar sun nuna adawada dokar hukuncin kisa da Isra'ila ta amince da ita kan Falasdinawa.
Dan Majalisa na jam'iyyar Democrat a Majalisar dokokin Amurka, Seth Moultonya caccaki Donald Trump kan yadda yake kokarin jefa rayuwar sojoji cikin hadari.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta tabbatar da cewa ta samu sako kan batun tsagaita wuta ta hannun masu shiga tsakani, ta ce za ta yi nazari a kai tukunna.
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya musanta abubuwan da ake yadawa game da kasar, ya bayyana cewa ba su taba tayar da yaki ba amma suka kare kansu.
Hukumomin agajin gaggawa na Isra'ila sunn tabbatar da cewa akalla mutane 14 ne suka samu raunuka sakamakon harin makami mai linzami a kusa da birnin Tel Aviv.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya jaddada goyon baya ga kungiyar Hezbolla a wata zungureriyar wasika da ya aika wa shugaban kungiyar, Nim Qassem.
Kasar waje
Samu kari