Jam'iyyar APC
Jarumar Kannywood kuma hadimar gwamnan jihar Kano, Asma'u Abdullahi, ya fice daga jam'iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya. Asma'u ta koma jam'iyyar APC.
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya maye gurbin shugaban alkalan jihar wanda Allah ya yi wa rasuwa bayan doguwar jinya ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024.
APC ta koka kan yadda Atiku Abubakar ke cigaba da sukan gwamnatin Bola Tinubu a kan tsadar rayuwa a Najeriya. APC ta ce ya kamata Atiku ya zamo dattijo.
APC ta ce ba ta jefa PDP cikin rikicin cikin gida ba a Najeriya. APC ta ce gwamnan PDP ya mayar da hankali wajen kawo cigaba maimakon zargin APC.
Yayin da ya rage ƴan kwanaki a fita zaɓen gwamna a jihar Ondo, tsohon ɗan majalisar tarayya da wasu manyan ƙusoshin PDP sun haɗe da Gwamna Aiyedatiwa a APC.
Jam'iyyar APC mai mulki ta mayar da martani da Gwamna Seyi Maminde na jihar Oyo wanda bisa dukkanin alamu ya fara shirin neman karawa da Tinubu a 2027
Za a ga jerin APC da aka ji sun soki gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya. Alal misali, sukar gwamnatin Bola Tinubu ne ya jawo Muhammad Ali Ndume ya rasa matsayinsa.
Jagora a jam'iyyar APC a jihar Osun ya bayyana cewa yankin Arewacin Najeriya ba zai ki sake zaben Shugaba Bola Tinubu ba kan dokar gyaran haraji.
Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kara himma wajen rage radadin da ake ciki.
Jam'iyyar APC
Samu kari