Jam'iyyar APC
Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya dauko hanyar cigaba wajen gina kasa bayan nasarar 2023 kuma ba za su bar yan adawa su mayar da kasa baya ba a 2027.
Tsagin jam'iyyar ADC ya zabi Dumebi Kachikwu a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar ADC takarar shugaban kasa a zaben 2027 maimakon Atiku Abubakar da sauransu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2027 bayan samun kuri’u kusan miliyan 11 a zaben fidda gwani da aka gudanar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya lashe jihohi 19 a zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, yayin da rahotanni suka nuna ya samu kuri’u 100% a jihar Borno.
Tsohuwar minista Nkeiruka Onyejeocha ta yabawa APC kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana, tana cewa hakan ya nuna goyon bayan jama’a ga Tinubu.
Gwamna Siminalayi Fubara ya rasa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da APC bayan zargin ya karya yarjejeniyar sulhu tsakaninsa da Nyesom Wike kan siyasar Rivers.
Tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, ya yi barazanar raba gari da jam'iyyar APC biyo bayan zaben fitar da gwanin da aka gudanar.
Kungiyar Pantamiyya Movement Brotherhood mai goyon bayan Farfesa Isa Pantami ta bayyana goyon bayanta ga Jamilu Isyaku Gwamna bayan zaben fidda gwani na APC a Gombe.
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya yi ikirarin cewa zaben fitar da gwanin APC na nuna har yanzu talakawan Najeriya na tare da shugaban kasa, Bola Tinubu.
Jam'iyyar APC
Samu kari