Jam'iyyar APC
Jam'iyyar adawa ta ADC ta mika wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tutar zama cikakken dan takara a zaben shugaban kasar da za a yi a 2027.
‘Yar Bola Tinubu kuma Shugabar Iyaloja-General ta Najeriya, Mrs Folashade Tinubu-Ojo, ta yi barazanar zanga-zanga kan sakamakon zaben fidda gwani na APC a Lagos.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa wanda ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC ya yi magana game da shirinsa kan Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya yi murabus daga APC bayan shan kaye a zaben fitar da gwani na kujerar sanatan Delta ta Tsakiya.
Sanata Ned Nwoko ya yi watsi da zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC da aka yi a jihar Delta. Ya ce APC ta juya masa baya duk da Ganduje ya masa alkawarin tikiti.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi ikirarin cewa akwai yan Najeriya da dam da za su zabi Bola Tinubu wadanda ba su yi rijistar jam'iyya ba.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sanar da cewa tun a lokacin sulhu aka yi da wajewa cewa gwamna Siminalayi Fubara ba zai nemi takara ba a zaben 2027.
A labarin nan, za a ji tsohon gwamnan Kano ya koro bayani game da yadda gwamna Abba ya rabu da su, da kuma tsarin da za a bi wajen fitar da dan takara a 2027.
Hon. Mustapha Dawaki, tsohon shugaban ma'aikatan shugaban APC na kasa ya sauya sheka zuwa NDC a Kano, Sanara Rabiu Kwankwaso ya tarbe shi a gidansa.
Jam'iyyar APC
Samu kari