Dandalin Kannywood
Bayan kwanaki ana ce-ce-ku-ce, Khadija mai bakin kiss ta fito ta wanke Momee Gombe daga zargin madigo. Khadija ta ce karyata shirga da ta ce tana da bidiyon Momee.
Rahama Sadau ta ce fim hanya ce ta isar da sakon rayuwa, ba kawai don daukaka ba, kamar yadda aka gani a wajen haska fim dinta na 'Mamah' a kasar Saudiya.
Mansura Isah ta shiga tsananin damuwa bayan 'yan damfara sun sace gaba daya kudin da ta mallaka a asusun bankunanta biyu. Tsohuwar jarumar ta ce yanzu ta talauce.
Fitacciyar jarumar TikTok a Arewacin Najeriya, Murja Ibrahim Kunya ta fitar da bidiyon sabuwar waya kirar iPhone 16 da ta saya. Mutane sun yi mata ca.
Fitaccen mawakin Kannywood, Auta Waziri ya na gayyata daukacin masoyansa zuwa daurin aurensa a ranar Juma'a, 6 ga watan Disambar 2024. Ya saki zafafan hotuna.
Fitaccen jarumar Kannywood, Teema Yola ta wallafa bidiyon da ake kyautata zaton shi ne na karshe na mawaki El-Muaz Birniwa kafin rasuwarsa a daren ranar Alhamis.
Allah ya yiwa fitaccen mawakin Kannywood, El'Muaz Birniwa rasuwa. An rahoto cewa ya rasu ne a daren ranar Alhamis. Jarumai da 'yan Kannywood sun yi alhini.
Mahaifiyar jarumar Kannywood, Rukayya Ahmad Aliyu, wadda aka fi sani da Ruky Alim ta rasu. Jarumai da masu shirya fina finan Hausa sun yi ta'ziyyar wannan rashi.
Jarumar Kannywood, Aishatul Umairah ta bayyana alakar da ke tsakaninta da mawaki Dauda Kahutu Rarara yayin da rade radi ke yawo na ya kai kudin sadakinta.
Dandalin Kannywood
Samu kari