Rashawa a gwamnatin Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta gurfanar da Yakubu Adamu, kwamishina a Bauchi gaban kotu.
Rahotanni kan shari'ar Chris Ngige sun jawo ce-ce-ku-ce yayin da EFCC ke binciken tsofaffin ministocin Buhari irin su Timipre Sylva, Malami da Hadi Sirika.
Kotu ta ki amincewa da bukatar beli da Abubakar Malami ya shigar, tana cewa zamansa a hannun EFCC ya halasta bisa ingantaccen umarnin wata babbar kotun.
Aliko Dangote ya kai ƙara ICPC kan shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, bisa zargin kashe sama da $7m wajen karatun ’ya’yansa a Switzerland. Ya nemi a kama shi.
Aliko Dangote ya bukaci a binciki shugaban NMDPRA Farouk Ahmed kan zargin biyan $5m kudin makarantar ‘ya’yansa a Switzerland. Ya ce kudin sun wuce albashin Farouk.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar EFCC ta fara shari'a da tsohon Ministan kwadago ta Najeriya, Chris Ngige a gaban kotu a kan zarge zargen rashawa.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce EFCC ta tsare shi ba tare da bayyana dalili ba bayan soke belinsa duk da cewa ya cika sharuddan da aka gindaya masa.
Abubakar Malami ya kwana a ofishin EFCC bayan tsawon tambayoyi kan binciken asusun banki 46 da ake zargin yana da alaka da su da wasu badakaloli a lokacin Buhari.
Majalisar Dattawa ta kira ministocin kudi, kimiyya da tsaro domin bayyana yadda shirin Safe School ya lalace bayan kashe dala miliyan 30 da biliyoyin naira.
Rashawa a gwamnatin Najeriya
Samu kari