
Muhammadu Buhari







Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce za su nunawa 'yan adawa cewa sun shirya a zaben 2027. Ya yi raddi wa Atiku da El-Rufa'i kan hadakar 'yan adawa.

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya jagoranci manyan 'yan APC zuwa gidan Buhari a Kaduna. Hakan na zuwa ne bayan Atiku, El-Rufa'i sun ziyarci Buhari.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa ziyarar da mutane ke kai wa taohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ba sabon abu ba ne saboda ya zama uban ƙasa.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi barkwanci a lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarce shi a Kaduna. Buhari ya cewa Pantami ya murmure.

Sanatan Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya ce Bola Tinubu ya kamata ya shiga damuwa idan tsohon shugaban kasa Buhari bai goyi bayansa ba musamman a zabe.

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ziyarar da Atiku da tsofaffin gwamnoni suka kai wa Buhari a Kaduna ba ta da alaƙa da siyasa ko batun 2027.

Yayin da yan adawa suka ziyarci Muhammadu Buhari a Kaduna, jiga-jigan APC a Kachia sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu da Gwamna Uba Sani a 2027.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi wanda ya rasu a ranar 3 ga watan Afrilun 2025 da muke ciki.

Jagora a NNPP ya yi zargin cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi takaicin yadda Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar kama mulkin Najeriya.
Muhammadu Buhari
Samu kari