
Jihar Benue







Gwamnatin jihar Benue ga ƙaryata rahoton da ake yaɗawa cewa tana nuna wariya ga wasu yan Majalisar dokoki masu goyon bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Sojojin Najeriya sun gwabza da 'yan ta'adda a Taraba da Benue a wani samame da suka yi. Sojojin sun kwato motar 'yan ta'adda da babur d wasu bindigogi.

Dan Majalisar Tarayya daga jihar Benue, Philip Agbese ya yabawa Bola Tinubu kan sabon kudirin haraji da ke gaban Majalisa inda ya ce yan Najeriya za su yaba masa.

Babbar kotu a jihar Benue ta rusa kwamitin da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya kafa domin magance rikicin APC a Benue. Kotun ta ce Ganduje ya karya doka.

'Yan ta'adda sun halaka kimanin mutane 30 tare da raunata sama da mutane 37 a garuruwan jihar Benuwai. An ce 'yan ta'addan sun kona gidaje da sace kayayyaki.

Wasu 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan wani matashin lauya a jihar Benue. 'Yan bindigan sun bi matashin lauyan har gida sannan suka bude masa wuta.

Gwamnan Benue ya yi karin mafi ƙarancin albashi zuwa N75,000 ga ma'aikata. Gwamnan ya ce ya kara albashi sama da yadda Tinubu ke biya a matakin tarayya.

Gwamnan Benuwai, Hyacinth Alia ya sanar da maido da antoni janar kuma kwamishinan shari'a kan kujerarsa bayan ya cika haruddan da aka gindaya masa.

Kungiyar MBF ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya maido tallafin man fetur a Najeriya lura da yadda miliyoyin yan kasa suka shiga mugun talauci da wahala.
Jihar Benue
Samu kari