Jihar Benue
Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya kaddamar da kwamitin dawo da kadarorin gwamnati waɗanda yake zargin Ortom da mukarrabansa sun yi sama da faɗi da su.
Shugabannin kananan hukumomi 23 da gwamnatin jihar Benue ta dakatar sun nunawa Gwamna Hyacinth Alia yatsa. Sun sha alwashi cewa ba zasu sauka daga kujerunsu ba.
Jam'iyyar PDP reshen Benuwai ta caccaki gwamnatin PDP karkashin mulkin gwamna Hyacinth Alia dangane da matakin da ya ɗauka kan ciyamomin kananan hukumomi 23.
Majalisar dokokin jihar Benue, ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar daga kan muƙamansu, bisa zargin almundahanar maƙudan kuɗaɗen al'umma.
A ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, majalisar dokokin jihar Benue ta ba da shawarar dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar kan zargin wawure kudade.
Rahoto daga Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, ya nuna cewa yanzu haka tsohon gwammnan jihar da ya sauka kwanan nan, Samuel Ortom, na tsare a ofishin EFCC.
Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace Malamin Coci a yankin karamar hukumar Ohimini ta jihar Benuwai ranar Alhamis da daddare.
Gwamnan jihar Benue Rev. Fr. Hyacinth Alia ya shirya dawo da kadarorin gwamnatin jihar waɗanda gwamnatin Samuel Ortom, ta tattara ta yi awon gaba da su a jihar.
Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia, ya soke duk wasu tsare-tsareda sauye-sauyen tsohon gwamna, Samuel Ortom, waɗanda ya yi gab da zai bar mulki .
Jihar Benue
Samu kari